ads

Home > Hukumar INEC ta nemi afuwar 'yan Najeriya sakamakon dage zabe da tayi

Hukumar INEC ta nemi afuwar 'yan Najeriya sakamakon dage zabe da tayi

Prof-Mahmood-Yakub.jpg

Hukumar zabe ta kasa INEC ta nemi afuwar 'yan Nigeria sakamakon dage zaben da tayi wanda aka  shirya gudanarwa a ranar Asabar.

An dage babban zaben shekarar 2019 ne sa'o'i kalilan kafin fara shi, inda aka dage shi zuwa ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Wani darakta a hukumar zaben kasar Festus Okaye ya ce har bayan karfe 12;00 na daren ranar Asabar hukumar tana da tabbacin za ta iya gudanar da zaben.

Jami'in ya ce sun samu matsala ne akalla a bakwai daga cikin jihohi 36 da ke fadin kasar.

Hukumar INEC ta dage babban zaben Najeriya zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu

Mista Festus ya ce hukumar zaben ta yi takaicin abin da ya faru kuma saboda haka tana neman afuwar 'yan Nigeria.

Daga nan ya ba da tabbacin cewa hukumar zaben ta dukufa wajen ganin ta gudanar da zaben kamar yadda aka tsara a mako mai zuwa.

Ya bukaci 'yan kasar da su ba hukumar goyon baya da hadin kai don ganin ta gudanar da sahihin zabe.

Domin samun makamantan wadannan labarai, shiga: hausapost.com.ngads

ads